Kasashen Afirka Na Cin Gajiyar Aikin Zamanintar Da Aikin Gona Na Sin
2023-11-16 12:27:54 CMG HAUSA
Innocent Mojidi dan kasar Najeriya ne mai shekaru 35 da haifuwa, ya taba zuwa kasar Sin sau biyu don samun horo a fannin aikin gona, yauzu yana noman shimkafa da masara a gonakinsa dake karkarar birnin Abuja hedkwatar Najeriya. Saboda kwarewar da ya samu, ya zama masanin aikin gona a garinsu. ‘Yan Afrika da dama ne kamar Innocent Mojidi suka zo kasar Sin don koyon dabarun aikin noma na zamani, matakin da ya taimaka musu wajen tinkarar matsalar karancin isasshen hatsi.
A cikin shekaru 10 da suka gabata bayan Sin da Afrika suka yi hadin gwiwa a fannin aikin noma, Sin ta kulla yarjeniyoyi 34 da kasashen Afrika da AU da AGRA a wannan bangare, da kuma yin mu’ammala kan samar da isasshen hatsi da rage talauci da tinkarar sauyin yanayi da sauransu. Ban da wannan kuma, ma’aikatar aikin noma da raya kauyuka ta kasar sin ta tura masananta fiye da 400 zuwa kasashen Afrika tare da horar da ‘yan Afrika fiye da dubu 10.
Ban da samar da dabaru na kimiyya da fasaha, Sin ta taimakawa kasashen Afrika wajen gina wasu manyan ababen more rayuwa a wannan fanni. Gwamnatin Sin ta tallafawa Najeriya wajen gina cibiyar raya aikin gona ta gwaji a Abuja kyauta, wannan cibiyar ta fitar da wani nau’in irin shimkafa samfurin Gawal R1, kuma an yi shekaru 5 ana shuka wannan iri a Najeriya, wanda ya samar da karin shinkafa tan miliyan 2, inda manoma fiye da dubu 200 suka ci gajiya. A cikin shekaru 10 da suka gabata, Sin ta taimakawa kasashen Afrika wajen gina cibiyoyin gwaji a fannin aikin noma 24, inda aka gabatar tare da yayata fasahohi fiye da 300 a wuraren, yawan karuwar hatsi da aka samu ya kai kashi 30% zuwa 60%, manoma kimanin miliyan 1 sun ci gajiyar wadannan fasahohi.
Yanzu, gwamnatin Sin na kara karfafa hadin gwiwa da kasashen Afrika a wannan fanni, kuma ta gudanar da dandalin hadin kan Sin da Afrika a fannin aikin gona karo na 2 a birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin daga ran 13 zuwa 15. Dandalin na da zummar habaka hadin kan bangarorin biyu, ta yadda za a kara inganta ayyukan gona a kasashen Afrika, tare da cimma muradun samun ci gaba nan da shekara ta 2030 a wannan bangare a kasashen Afrika.
Ayyukan hadin kai a bangaren aikin noma karkashin shirin hadin kan kasashe masu tasowa da shawarar “ziri daya da hanya daya” sun samarwa kasashe masu tasowa musamman ma kasashen Afrika tallafin manyan ababen more rayuwa a fannin aikin noma da kudade da fasahohi da hatsi da sauransu, matakan da za su taimaka musu wajen samun bunkasuwa da dogara da karfin kansu. Labarin Mojidi da cibiyar gwaji ta fasahohin aikin noma dake Abuja sun zama misali ta fuskar hadin kan Sin da Afrika. Ana sa ran cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, bangarorin biyu za su samu karin ci gaba a wannan fanni. (Mai zana da rubuta: MINA)