logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya amince da kudurin tsagaita wuta don samar da agajin jin kai a Gaza

2023-11-16 09:29:29 CMG Hausa

A jiya Laraba ne kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri na neman gaggauta tsagaita wuta don samar da agajin jin kai na tsawon lokaci a zirin Gaza.

Kuduri mai lamba 2712 ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta don samar da ayyukan jin kai na “isassun kwanaki” a ko ina cikin zirin Gaza don ba da damar isar da agajin jin kai cikin sauri, da aminci, kuma ba tare da cikas ba don saukake ci gaba da samar da kayayyaki da ayyuka masu mahimmanci a sassan Gaza, da kuma ba da damar gudanar da ayyukan ceto, ciki har da yara da suka bace a cikin gine-ginen da aka rushe, da fitar da marasa lafiya da yara da suka ji rauni da masu kula da su. (Yahaya)