logo

HAUSA

Jami’in MDD: Sin babbar mai taka rawa ce wajen magance gibi a fannin cin gajiyar kafar Intanet a duniya

2023-11-16 11:05:57 CMG Hausa

Babban jami’i mai kula da fasahohin zamani na shirin raya kasashe na MDD (UNDP) Robert Opp, ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance babbar mai taka rawa, wajen magance gibin dake akwai a fannin cin gajiyar Intanet a duniya.

Robert Opp ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wannan mako, yayin taron kolin yanar gizo na duniya da aka yi a Lisbon na kasar Portugal cewa, fasaha da kirkire-kirkire na da muhimmanci wajen fuskantar wannan kalubale.

Ya ce, a bayyane yake kasar Sin tana da karfin fasahar kere-kere, da gano sabbin hanyoyin da za su sa fasahar ta zama mai araha kuma a wadace. Kana sun fahimci lokacin da ake ganin yadda fasahar Intanet, za ta jagoranci shirin samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.

UNDP, kungiyar samar da ci gaba mai dorewa ta MDD, tana aiki a cikin kasashe 170 don kawo karshen talauci da rashin daidaito da magance matsalar sauyin yanayi.

Taron kolin yanar gizon dake zama daya daga cikin manyan tarukan fasaha na duniya, ya karbi bakuncin mutane 70,236 daga kasashe 153, da ma sabbi 2,608 da ke halartar taron na bana a karon farko. (Ibrahim)