logo

HAUSA

Masanin Najeriya: Ziyarar za ta ba da ma’ana kwarai da gaske ga kasashen Sin da Amurka

2023-11-16 16:50:42 CMG Hausa

Yayin da yau Alhamis aka shiga rana ta biyu ta ziyarar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ke kan yi a kasar Amurka, masana harkokin siyasa da na tattalin arzikin duniya na ci gaba da bayyana tasirin da wannan ziyara ke da ita ta fuskoki da dama.

Kasashen Sin da Amurka muhimman kasashe ne da suke zama mizanin haska makomar tattalin arzikin duniya da na siyasa.

Da yake tsokaci kan ziyarar a ganawarsa da wakilinmu a tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai, wani masani a kan harkokin diplomasiyyar duniya Malam Isma’il Ahmed ya ce, hakika ziyarar ta zo da ba za ta ganin yadda alakar kasashen biyu ta yi tsami a ’yan shekarun nan.//////

 

“Ziyarar za ta ba da ma’ana kwarai da gaske ta fuskar diplomasiyya duba da karfin tattalin arziki da dukkan bangarorin guda biyu suke da shi. Na farko Amurka ta fi kowacce kasa karfin tattalin arziki a duniya, na biyu ita kuma kasar Sin ita ce karfin tattalin arzikin ta yafi na kowacce kasa saurin habaka a duniya. Kowanne yana bukatar kowane a cikinsu, saboda haka shekara shiddan nan da shugaba Xi bai kai ziyara Amurka ba, abubuwan da suka biyo baya ta fuskar tattalin arziki tun lokacin tsohon shugaban Amurka Donald Trump da aka rinka kakkabawa juna takunkumi da kuma mayar da martani ta fuskar tattalin arziki din da kasashen guda biyu suka yi, hakan ya sanya kowanne bangare ya ja daga kuma yana shakka kowanne bangare. Dole ne ta fuskar shi shugaba Xi zai nemi ya yi amfani da damar da take hannunsa domin ya nemi karin masu zuba jari musamman a wannan taron na Asia Pacific din nan da za a yi, sannan ita kuma Amurka ba za ta so ta nuna cewa shugaba Xi yana da wani tasiri sosai ta fuskar tattalin arzikinta ba, to amma kuma a kalaman shugaba Biden ya nuna cewa, lallai suna bukatar juna, tasirin zai kasance ta fuskar tattalin arziki saboda kowa yana bukatar kowa, amma ba na tunanin cewa ta fuskar siyasa, ziyarar za ta sanya kowa ya rage karfin abun da yake da shi musamman nuna goyon bayan da Amurka take yi musamman ga yankin Taiwan da kuma ziyarar da mataimakiyar shugabar Amurka da sauran maganganu da su suke ta yi kan fafutukar a kan  Taiwan din nan yana konawa kasar Sin rai kwarai da gaske, sai kuma ta fuskar ita kanta kasar Sin da ba ta goyon bayan wasu manufofin Amurka musamman a Turai da majalissar dinkin duniya, saboda haka ta fuskar siyasa ba lallai ba ne a samu saukin dangantaka tsakanin kasashen biyu, amma ta fuskar tattalin arziki sabo da kowa yana bukatar kowa za ka ga cewa an samu wani ci gaba kwarai da gaske.” (Garba Abdullahi Bagwai)