logo

HAUSA

An cimma matsaya kan batutuwa sama da 20 a taron San Francisco

2023-11-16 19:39:15 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta ce shugaba Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden, sun yj tattaunawar keke da keke mai zurfi a jiya Laraba, kuma hanyar da ta dace da kyautata dangantakarsu, ta kara fayyace nauyin dake wuyan manyan kasashen tare da samar da "burin San Francisco" domin kyautata makomarsu.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Alhamis. 

A cewar Mao Ning, wannan kyakkyawar ganawa ce mai ma'ana dake da muhimmiyar tasiri mai kyau. Tana mai cewa, batu ne mai muhimmanci ga duniya, haka kuma nasara ce ga tarihin dangantakar kasashen biyu.

Mao Ning ta jaddada cewa, tattaunawa da hadin gwiwa ita ce kadai zabi mai kyau ga kasashen biyu. Kuma ya kamata tattaunawar ta San Francisco ta zama mafarin kyautata dangantakarsu. Bugu da kari, akwai bukatar bangarorin biyu su karfafa tubalin dangantakarsu, da gina ginshikin hulda da juna cikin aminci da karko kuma bisa alkibla mai dorewa. (Faiza Mustapha)