logo

HAUSA

Ofishin jakadancin Sin ya ba da gudummawar kayayyaki ga gidan marayu da Sinawa ke taimakawa a Zimbabwe

2023-11-15 11:06:52 CMG Hausa

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Zimbabwe ya ba da gudummawar kayayyakin abinci, da na rubutu da sauransu, ga gidan marayu na Hossana Love in Africa da kasar Sin ta ba da taimako.

Jakadan Sin dake Zimbabwe Zhou Ding ne ya mika kayayyakin ga gidan marayun a harabarsa da ke unguwar Hatcliffe mai nisan kilomita 25 a wajen Harare, babban birnin kasar Zimbabwe.

A shekarar 2016 ne, ofishin jakadancin kasar Sin da al’ummar Sinawa da ke Zimbabwe, suka fara ba da gudummawa ga gidan marayun, kuma tun daga wancan lokaci zuwa yanzu, suke taimakawa.

Jami’ar dake kula da gidan marayun, Sharon Chivambo, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, suna godiya da tallafin da Sinawa ke ba su, amma suna bukatar karin tallafi, don gina karin azuzuwan karatu, da kara inganta tsarin samar da ruwa. (Ibrahim)