logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da kwamatin wocin gadi kan taro akan sauyin yanayi na duniya da za a gudanar COP28

2023-11-15 16:18:11 CMG Hausa

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da kwamatin wocin gadi da zai fito da bukatun Najeriya yayin babban taron duniya kan sauyi yanayi na 2023 COP28 wanda za a gudanar a hadaddiyar daular larabawa a tsakanin 30 ga wannan watan zuwa 12 ga watan gobe na Disamba.

A lokacin daya ke kaddamar da `yan kwamatin a birnin Abuja, mataimakin shugaban kasan yace yana daga cikin alhakin dake kan yan kwamatin samar da wata taswirar da zata kai ga Najeriya cin gajiyar taron musamman kirkiro da dabarun adana makamashi.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Sanata Kashim Shettima yace ya zama wajibi Najeriya ta kimtsa sosai  gabannin taron domin tabbatar da ganin cewa dukkan burikan kasar a game da kaucewa kalubalen sauyin yanayi sun kai ga cika.

Yace zai zama abun kunya wakilan Najeriya a wajen taron su gaza dawowa da fa`idojin dake tattare da wannan mahimmin taro na COP28 wanda zai taimaka wajen fito da wasu sabbin dabarun adana makamashi.

Yace Najeriya na dakon tallafin kasashe da masu saka jari da zasu shigo kasar domin kulla yarjeejniyar samar da batira masu adana makamashi.

A jawabin sa shugaban kwamatin kuma ministan Muhalli na tarayyar Najeriya Alhaji Balarabe Abbas Lawan, ya tabbatar dacewa kwamatin nasu zai nazarci kundin bayanan taron da nufin zakulo wasu mahimman fasahohin zamani da suka hada da samar da batiran adana wuta wanda da zasu kawo karshen matsalolin karancin wuta a Najeriya.

“ Da man dai babban abun da muke son cimmawa shine tabbatar da ganin annobar yawan katsewar wutan lantarki a Najeriya ya kau, abun da zamuyi kokarin samar shine wani runbu adana makamashi wanda ke da kamanceceniya da abun da ake kira UPS wanda da zarar an dauke wuta shi kuma zai cigaba da bada haske, a takaice dai baza a sake samun daukewar wuta ba” (Garba Abdullahi Bagwai)