logo

HAUSA

Sin: Kamata ya yi iznin da MDD za ta bayar ya dace da halin da ake ciki

2023-11-15 15:56:11 CMG HAUSA

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya gabatar da jawabi a taron shekara-shekara da aka yi da kwamishin ‘yan sanda na kwamitin sulhu na MDD a jiya Talata, inda ya nanata wajibcin MDD da ta ba da izni bisa halin da ake ciki.

Zhang Jun ya ce, aikin wanzar da zaman lafiya da MDD ke gudanarwa na fuskantar mawuyancin hali da kalubaloli da ba a taba gani ba, don haka akwai bukatar yi wa wadannan ayyuka kwaskwarima, ta yadda ‘yan sandan wanzar da zaman lafiya za su taka rawar da ta dace don tinkarar sabon halin da ake ciki.

Zhang Jun kuma ya ba da shawarwari guda shida, wato wajibi ne iznin da MDD za ta bayar ya dace da halin da ake ciki, da kulla dangantaka mai kyau da kasashen da aka tura da jami’an, da kara karfinsu na wanzar da zaman lafiya, da tabbatar da tsaron masu aikin kiyaye zaman lafiya, da kuma kwarewa da karfafa gwiwar ma’aikata mata wajen takar rawa ta musamman, da tinkarar kalubaloli na sabbin fasahohi.

Zhang Jun ya kara da cewa, kasar Sin na fatan mambobin kwamitin sulhu za su yi amfani da wannan taro, wajen yin musayar ra'ayi mai zurfi, ta yadda za a mai da hankali kan kara karfin ‘yan sandan wanzar da zaman lafiya, don kara hadin kai wajen ba da iznin da ya dace, lamarin da zai taimaka wajen kara taka rawa a aikin shimfida zaman lafiya da tabbatar da tsaro a fadin duniya tare. (Amina Xu)