Ziyarar shugaban kasar Sin a kasar Amurka za ta kawo albishiri ga duk duniya
2023-11-15 07:22:03 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping na halartar taron kolin kasashen Sin da Amurka, da taron shugabannin tattalin arzikin Asiya da Fasifik (APEC) karo na 30 da dake gudana San Francisco. Kafin a kai ga wannan mataki mai nuni da murmurewar dangantakar kasashen biyu da ta yi tsami a cikin ‘yan shekarun nan har ma ta kai ga “yakin mummuke”, Manyan jami’an Amurka da suka hada da da suka hada da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, da sakatariyar baitulmali Janet Yellen da sakatariyar kasuwanci Gina Raimondo suka ziyarci kasar Sin bi da bi, a matakin da ke nuni da sharan fage domin wannan ganawa ta San Francisco.
Makasudin wannan ganawa tsakanin shugabannin kasashen Amurka da Sin shi ne, shawo kan gasa, da hana afkuwar rikici, da tabbatar da yin mu’amala yadda ya kamata. Duk da cewa Kasar Sin ba ta tsoron gasa, amma tana adawa da yin amfani da kalmar gasa wajen fayyace dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.
Ana sa ran halartar shugaba Xi a taron kolin Sin da Amurka da taron kolin kungiyar APEC zai tabbatar da fahimtar ci gaban kasar Sin dake dauke da tarihi mai muhimmanci, da taimakawa kasashen duniya samun karin wadanda za su jagoranci ci gaban duniya ta hanyar yin amfani da tsarin zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Ibrahim Yaya, Muhammed Yahaya, Sanusi Chen)