logo

HAUSA

An gudanar da taron APEC kan kirkire-kirkire maras gurbata muhalli

2023-11-14 10:12:23 CMG Hausa

A jiya ne, a birnin San Francisco na jihar California ta kasar Amurka, aka gudanar da wani babban taron dandalin tattaunawa, kan batutuwan da suka fi dacewar hanzarta amfani da sabbin manufofi da fasahohin da za su kai ga farfado da tattalin arzikin kasashen kungiyar yankin Asiya da tekun Pasifik (APEC).

Taron wanda kwamitin kula da makamashi mai tsafta na kasashen Amurka da Sin da cibiyar makamashi mai dorewa ta APEC suka shirya, ya samu halartar masana, da wakilai daga mambobin APEC, da shugabannin kasuwanci daga manyan kamfanonin samar da makamashi mai tsafta a duniya.

Tsohon sakataren makamashi na Amurka kuma mutumin da ya lashe lambar yabo ta Nobel Steven Chu da shugaban hukumar makamashi ta California, David Hochschild sun gabatar da muhimman jawabai a dandalin.

A jawabinsa Steve Chu ya bayyana ra'ayin cewa, ya kamata kasashen Amurka da Sin su ci gaba da yin mu'amala da juna kan batun da ya shafi sauyin yanayi.

A nasa bangare David Hochschild, wanda ya ziyarci kasar Sin kwanan baya tare da gwamnan California Gavin Newsom, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, akwai babbar dama ta inganta hadin gwiwar jihar Golden da kasar Sin wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi.

Ya ce, kasar Sin ta cancanci yabo mai yawa, kasancewarta babbar kasuwa kana mai kera baturan samar da wutar lantarki daga hasken rana da iska, musamman iskar teku.

Za a dai gudanar da taron makon shugabannin APEC na shekarar 2023 ne, a birnin San Francisco na kasar Amurka, daga ranar 11 zuwa 17 ga watan Nuwamba, bisa taken "Samar da makoma mai dorewa ga kowa." (Ibrahim Yaya)