Kwararre dan kasar Croatia : "Double 11" ya nuna juriyar tattalin arzikin kasar Sin
2023-11-14 10:29:45 CMG Hausa
Yawan kunshin kayayyaki da aka tattara a lokacin "Double 11", bikin cin kasuwar kasar Sin mai kama da Black Friday, ya tabbatar da juriya da farfadowar tattalin arzikin kasar Sin daga annobar COVID-19, kamar yadda Kresimir Macan, wani kwararre a fannnin tattalin arziki dan kasar Croatia, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wata hirar da aka yi da shi a ranar Litinin.
"Mutane da yawa sun yi ikirarin cewa tattalin arzikin kasar Sin na fuskantar munanan yanayi, kuma yawan kayayyakin da take samarwa ya ragu, yayin da aka samu akasin hasashen da aka yi. Sai dai sabbin bayanai sun karyata hakan, kuma sun nuna juriya da farfadowar tattalin arzikin kasar", a cewar Macan.
Hukumar kula da sakonni ta kasar Sin ta ce, daga ranar 1 zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, kamfanonin aika sakonni a duk fadin kasar sun tattara kimanin kunshin kayayyaki biliyan 5.26, wanda ya karu da kashi 23.22 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. A ranar 11 ga Nuwamba kadai, an tattara jimillar kunshin kayayyaki miliyan 639, wanda ya ninka da kashi 1.87 na adadin kasuwancin yau da kullun, wanda ke wakiltar karuwar kashi 15.76 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.
An yi hasashen GDP na kasar Sin zai karu da kaso 5.4 cikin dari a shekarar 2023, a cewar sanarwar da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar a ranar 7 ga watan Nuwamba. Macan ya yi nuni da cewa, sauran cibyoyin hada-hadar kudi kamar JP Morgan, da USB da Bankin Deutsche, sun daga matsayin hasashen ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a bana.
"Duk wadannan suna nuni ne da karkon tattalin arzikin kasar Sin," a cewar Macan, ya kuma kara da cewa farfadowar na da kyau ga kasar Sin da ma duniya baki daya. (Muhammed Yahaya)