logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun yi nasarar halaka 'yan bindiga 3 a wani samame da suka kai

2023-11-14 10:23:05 CMG Hausa

Rahotanni daga Najetiya na cewa, a baya-bayan nan sojojin kasar sun yi nasarar halaka 'yan bindiga a kalla uku, a wani samame da suka kai a jihar Kaduna da ke yankin arewacin kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojojin dake Kaduna Musa Yahaya, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar, inda ya ce a ranar Lahadin da ta gabata ne, sojojin suka yi artabu da 'yan bindigar a wani daji dake karamar hukumar Kajuru, lamarin da ya yi sanadiyar raunata da dama daga cikin 'yan bindigar.

A wani lamari makamancin wannan kuma, rundunar 'yan sandan jihar Katsina dake arewacin kasar, a ranar Lahadin da ta gabata ta yi nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Jibia, inda ta yi nasarar ceto a kalla mutane uku.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Aliyu Abubakar Sadiq, ya shaidawa manema labarai a birnin Katsina jiya Litinin cewa, hukumar tsaro ta kai dauki gaggawa ga wani kira da aka yi mata, game da harin da 'yan bindigar suka kai wani kauye da yammacin ranar Asabar.

Abubakar-Sadiq ya ce, tawagar 'yan sandan ta killace dazukan da ke kewayen wurin, inda ta yi nasarar kubutar da wadanda harin na ranar Lahadin da ta gabata ya rutsa da su, yayin wani bata kashi da 'yan ta’addan.

Hare-haren dauke da makamai, na zama babbar barazanar tsaro a yankunan arewaci da tsakiyar Najeriya, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da kuma yin garkuwa da mutane a 'yan watannin nan. (Ibrahim Yaya)