logo

HAUSA

Za a dawo da alakar sufurin jiragen sama kai tsaye tsakanin Najeriya da kasar Aljeriya

2023-11-14 10:07:43 CMG Hausa

Ministan sufurin jiragen sama na tarayyar Najeriya Mr. Festus Keyamo ya ce, shirye-shirye sun yi nisa wajen kammala sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Najeriya da kasar Aljeriya wajen sufurin jirage kai tsaye tsakanin kasashen biyu.

Ministan ya tabbatar da hakan ne lokacin da wakilan gwamnatin Algeria suka ziyarce shi a birnin Abuja bisa jagorancin jakadan Aljeriya a Najeriya .

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.