Kasar Sin ta bukaci kasa da kasa su mara baya wajen kawar da makaman nukiliya daga Gabas ta Tsakiya
2023-11-14 10:42:30 CMG Hausa
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira da a kara kokarin mara baya wajen tabbatar da kawar da makaman nukiliya daga yankin Gabas ta Tsakiya.
A cewar Geng Shuang, bisa la’akari da yanayin da ake ciki, ya kamata kasa da kasa su kara kokarin goyon bayan tabbatar da kawar da makaman nukiliya da sauran makaman kare dangi daga Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa batu ne na gaggawa dake da muhimmanci ga inganta sulhu da hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin tare da wanzar da zaman lafiya.
Da yake jawabi ga zama na 4 na taro kan kawar da makaman nukiliya da sauran makaman kare dangi daga yankin Gabas ta Tsakiya, Geng Shuang ya ce makaman su ne musabbabin karancin aminci tsakanin kasashen yankin, lamarin dake yin tsaiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin.
Ya kara da cewa, kasar Sin na goyon bayan dabarar amfani da nukiliya wajen tsaron kai, yana mai cewa, kasarsa za ta ci gaba da bayar da gudunmuwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma a shirye take ta hada hannu da sauran kasashe yayin wannan taro, domin cimma matsaya da karfafa samar da yankin Gabas ta Tsakiya da babu makaman nukiliya a cikinsa. (Fa’iza Mustapha)