logo

HAUSA

Mutane kimanin biliyan 3.5 na fama da matsalar baki

2023-11-13 10:06:02 CMG Hausa

 

Masu karatu, ko kuna fama da matsalar lafiyar baki? Hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta kaddamar da rahoton cewa, yanzu kimanin mutane biliyan 3.5 ne a duniya suke fama da cututtukan da suka shafi baki, wato cututtukan da suka shafi baki na addabar kusan rabin jimillar mutanen duniya. Duk da cewa, mutane na iya kare kansu daga kamuwa da cututtukan da suka shafi baki ne ta hanyar yin rigakafi.

Hukumar WHO ta bayyana cewa, a matsayin wani babi da ke cikin rahotannin hukumar masu kunshe da alkaluma daban daban, wannan shi ne irin wannan rahoto da aka wallafa a karo na farko mai taken “yanayin lafiyar baki a duniya” inda ya yi cikakken bayani kan kalubaloli da damammakin da ake fuskanta wajen kula da lafiyar bakin dan Adam a duniya.

Rahoton ya ce, cututtuka masu nasaba da baki, cututtuka ne da ba sa yaduwa tsakanin mutane, amma suna addabar yawan mutane har kimanin biliyan 3.5 a duniya, adadin da ya fi jimillar masu fama da manyan cututtuka marasa yaduwa guda 5 yawa har biliyan 1.

Mene ne manyan cututtuka marasa yaduwa guda 5? Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, wadannan su ne cuttukan tunani, cututtukan da ke shafar jijiyoyin zuciya, ciwon sukari, cututtukan da ke shafar tsarin sassan jikin dan-adam masu taimakawa numfashi, da ciwon sankara

A cewar rahoton, cututtukan baki da suka fi addabar mutane su ne rubewar hakora, munanan cututtukan da ke shafar gindin hakora, faduwar hakora da sankarar baki. Ciwon rubewar hakora ya fi addabar mutane masu yawa, wadanda yawansu ya kai biliyan 2.5. Munanan cututtukan da ke shafar gindin hakora, muhimman dalilai ne da suke haifar da faduwar baki dayan hakora, wadanda suke shafar mutane kimanin biliyan 1. Haka kuma a ko wace shekara mutane kimanin dubu 380 ne suka kamu da ciwon kansa a baki.

Ban da haka kuma, karuwar adadin masu fama da cututtukan baki tana karuwa a duniya. Cikin shekaru 30 da suka gabata, yawan masu fama da cututtukan baki ya karu da biliyan 1 a duniya.

An dade ana kau da kai daga kula da lafiyar baki, duk da cewa, ana iya yin rigakafin kamuwa da wasu cututtukan dake da nasaba da baki.

Rahoton ya nuna cewa, kashi 3 cikin kashi 4 na masu fama da cututtukan baki suna zama ne a kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga. Hukumar WHO ta yi nuni da cewa, muhimman dalilai 2 da suka sanya karuwar adadin masu fama da cututtukan baki su ne, kashe makudan kudade domin samun jinya da kuma karancin na’urori ko kayayyakin aiki da likitocin hakora za su yi amfani da su a hukumomin kiwon lafiya a mataki na farko, musamman ma a kasashe masu fama da talauci.

Hukumar ta WHO ta shawarci gwamnatocin kasa da kasa da su tanadi aikin ba da hidimomin kula da lafiyar baki cikin adalci, cikin shirin raya kasa da kuma tsarin kiwon lafiya na mataki na farko. (Tasallah Yuan)