logo

HAUSA

Ziyarar Xi ta APEC Na Nuni Da Kyakkyawar Sakamakon Yunkurin Daidata Dangantakar Sin da Amurka

2023-11-13 17:26:02 CMG Hausa

Bisa gayyatar da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron kolin kasashen Sin da Amurka, da taron shugabannin tattalin arzikin Asiya da Fasifik (APEC) karo na 30 da aka shirya gudanarwa a wannan mako a San Francisco. Kafin a kai ga wannan mataki mai nuni da murmurewar dangantakar kasashen biyu da ta yi tsami a cikin ’yan shekarun nan har ma ta kai ga “yakin mummuke”, bari mu waiwayi kadan daga cikin mu’amalolin baya-bayan nan da suka wakana tsakanin kasashen biyu kawo yanzu.

Tun daga watan Yunin bana ne manyan jami'an Amurka da suka hada da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, da sakatariyar baitulmali Janet Yellen da sakatariyar kasuwanci Gina Raimondo suka ziyarci kasar Sin bi da bi. Bugu da kari, tattaunawar da aka yi tsakanin wakilin musamman na kasar Sin kan sauyin yanayi Xie Zhenhua da takwaransa na Amurka John Kerry a jihar California ta samu sakamako mai kyau. Daga bisani kasashen biyu sun kafa kungiyoyin harkar tattalin arziki da na kudi da sauran hanyoyin musaya da hada-hadar kudi da cinikayya.

A karshen watan Oktoba kuma, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai ziyara kasar Amurka, inda ya gana da Biden, ya kuma tattauna da wasu manyan jami'an siyasa, da masu ruwa da tsaki da ’yan kasuwa na Amurka. Kazalika, He Lifeng, mataimakin firaministan gwamnatin kasar Sin, kana shugaban kwamitin harkokin tattalin arziki da kasuwancin Sin da Amurka na kasar Sin, shi ma ya ziyarci Amurka daga ranar 8 zuwa 12 ga wannan watan Nuwamba.

A karon farko, Amurka ta aika da wata babbar tawaga zuwa bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na shida (CIIE) da aka kammala a Juma’ar makon jiya. Ana ci gaba da yin mu'amala mai zurfi, kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta nuna alamun murmurewa.

Ginshikin alakar Sin da Amurka na dogaro ne da mu’amala tsakanin al’umman kasashen biyu. Kama daga ’yan kasuwan Amurka dake ziyara a kasar Sin, zuwa shirin "Bond with Guling: dandalin sada zumunta tsakanin Sin da Amurka na shekarar 2023," da kuma tawagar wakilan Flying Tigers na Amurka da suka ziyarci kasar Sin, duka wadannan mu’amaloli sun nuna kyakkyawar fahimta da zurfafa zumunci, wanda hakan ya kara karfafa zumunci da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Ana sa ran halartar shugaba Xi a taron kolin Sin da Amurka da taron kolin kungiyar APEC zai tabbatar da fahimtar ci gaban kasar Sin dake dauke da tarihi mai muhimmanci, da taimakawa kasashen duniya samun karin wadanda za su jagoranci ci gaban duniya ta hanyar yin amfani da tsarin zamanantarwa irin ta kasar Sin.

A gun taron kungiyar APEC da za a yi, kasar Sin za ta ci gaba da daukar nauyin da ya rataya a wuyanta a matsayinta na babbar kasa, da kokarin tabbatar da cewa kasuwanni masu tasowa da kasashe masu tasowa sun fi samun wakilci, da damar bayyana ra’ayoyinsu a harkokin duniya, da kuma sa kaimi ga ci gaba da kyautata tsarin mulkin duniya. (Muhammed Yahaya)