logo

HAUSA

Fadar Shugaban Falasdinawa ta yi watsi da yunkurin Isra’ila na “rabe Gaza da gabar yammacin kogin Jordan”

2023-11-13 10:30:18 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne fadar shugaban kasar Falasdinu ta yi watsi da yunkurin Isra’ila na “rabe Gaza da gabar yammacin kogin Jordan”, tana mai cewa yin hakan “ba zai haifar da tsaro da kwanciyar hankali ga kowa ba”.

A cikin wata sanarwar da kakakin fadar shugaban kasar Nabil Abu Rudeineh ya fitar, ya jaddada cewa Gaza wani bangare ne na yankin Falasdinu da ke karkashin ikon kungiyar ‘yantar da Falasdinu (PLO).

Abu Rudeineh ya ce yunkurin da Isra’ila ke yi na raba Gaza da gabar yammacin kogin Jordan ba zai yi nasara ba, kuma ba za a amince da shi ba, komai matsin lamba ko barazana.

Falasdinawa da dama ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila suke ci gaba da kaiwa Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a daidai lokacin da tsarin kiwon lafiya ya durkushe a yankin.

Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza a ranar Lahadi ya sanar da cewa, adadin wadanda suka mutu a hare-haren Isra’ila ya haura 11,180, ciki har da yara da mata kusan 8,000, tare da jikkata sama da 28,000. (Yahaya)