logo

HAUSA

Kasashen duniya na da ra’ayi daya kan hanyar zamanantar da kasar Sin da kwanciyar hankali da ci gaban Asiya da tekun Fasifik

2023-11-13 16:10:30 CMG Hausa

Yanzu haka, duniya na fuskantar tarin batutuwa na rashin tabbas, kuma dukkan bangarori na sa ran yankin Asiya da tekun Fasifik, zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa tare da jagorantar ci gaban tattalin arzikin duniya.

Tsohuwar shugabar kasar Philippines, Gloria Macapagal Arroyo, ta yi imanin cewa, yayin da ake fuskantar karuwar sauye-sauye masu sarkakiya kuma cikin sauri a duniya, kasar Sin na neman sabuwar hanyar ci gaba. Ta ce kasar Sin ta riga ta tabbatar da cewa ita ba abokiyar takara ba ce, abokiya ce ta neman ci gaba, inda take samar da kasuwanni da taimakon jari da fasahohi ga kasashe masu tasowa.

Shi kuma dan majalisar gudanarwa na kasar Singapore, Goh Chok Tong cewa ya yi, duniya baki daya, ta ci gajiyar ci gaban kasar Sin, musamman ma kasashen yankin Asiya da tekun Fasifik.

A nasa bangare, tsohon firaministan Kyrgyzstan Djoomart Otorbayev, cewa ya yi kasar Sin ta kasance mai goyon bayan hadin gwiwar moriyar juna da dukkan abokan huldarta ta hanyar bude kofarta ga sassan duniya.

Tsohon jakadan Singapore a MDD kuma marubuci, Kishore Mahbubani, ya bayyana cewa, dadadden tarihi da al’adun kasar Sin sun raya ra’ayin neman ci gaba cikin lumana na kasar Sin. Ya ce yayin da ta kara fadada bude kofa ga sassan duniya, wannan ra’ayi zai aka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da ma duniya baki daya. (Fa’iza Mustapha)