logo

HAUSA

Julie: Zan kara samun damammaki masu yawa sakamakon ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da tsibiran Solomon

2023-11-13 20:29:52 CMG Hausa

[!--begin:htmlVideoCode--]c83f0ab7131f483f9d7932c4f6d7f48a,2,1,,news[!--end:htmlVideoCode--]

A baya bayan nan ne kasar Sin da tsibiran Solomon, suka ba da sanarwar kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni irin ta mutunta juna, da neman ci gaba tare a sabon zamani, kana kuma suka rattaba hannu kan wasu takardu na hadin gwiwa da suka shafi hadin gwiwar raya kasa, da kasuwanci, da gina ababen more rayuwa, da zirga-zirgar jiragen sama, da ilimi, da ayyukan 'yan sanda, kwastan da kuma nazarin yanayi da dai sauransu.

Ga Julie, daliba 'yar asalin tsibirin Solomon dake karatu a wata jami'a a lardin Guangdong na kudancin kasar Sin, bunkasuwar dangantakar kasashen biyu na kara mata damammakin ci gaba. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah mai suna Julie, ‘yar kasar Solomon.

"Shin kun san tsibiran Solomon? Kasa ce mai tsibirai a tekun Pacific kuma kasa ce mai tasowa.”

Julie, ‘yar asalin kasar Solomon daga Jami’ar Nazarin Harsunan Waje da Harkokin Cinikayyar Waje ta Guangdong, ta gabatar da garinsu ga manema labaran mu da farko. Gaskiya, a matsayinta na kasa mai nisan kilomita dubbai, kuma ta kafa huldar diflomasiyya da kasar Sin na tsawon shekaru hudu kacal, kasar Solomon har yanzu tana da dan nisa da ban mamaki ga Sinawa da dama. Julie ta ce saboda launin fatarta mai duhu, bayan da ta zo kasar Sin, Sinawa da dama sun tambaye ta ko ta fito ne daga Afirka.

“Na ce ni yar tsibiran Solomon ce, ba su san inda kasar take ba, sai na gaya musu cewa, tana kusa da Ostiraliya, sannan suka gane. Ina ganin jama'ar kasar Sin suna da kirki, kuma mai nuna kauna da son taimakawa saura, musamman ma idan aka neman hanya daga wajensu.”

Tsibiran Solomon, dake kudu maso yammacin Tekun Pasifik, na da manyan tsibirai da kanana fiye da 900. Kasar na da yanayin dazuzzuka kuma tana zafi duk shekara. Julie ta ce, sannu a hankali tana kokarin sabawa da yanayi, da abincin lardin Guangdong.

“Na saba da yanayin zafi. Amma abin da nake bukatar daidaitawa shi ne lokacin sanyi. A gare ni, lokacin sanyi a Guangzhou yana da tsanani. Ina son cin kayan zaki da shan shayi na safe irin na Guangdong. Abincin da na fi so na kasar Sin a halin yanzu shi ne dafaffiyar dambu wato dumplings a Turance, na fi son irin mai kunshe da ganyaye a ciki, naman sa kuma yana da kyau.”

Julie ta yi karatun kasuwanci na kasa da kasa a Jami’ar Nazarin Harsunan Waje da Harkokin Cinikayyar Waje ta Guangdong. Ta ce ta zabi wannan fannin karatu ne saboda fatanta na bayar da gudummawa wajen bunkasa harkokin cinikayyar waje a tsibiran Solomon.

“Wannan fannin karatu ne mai kyau ga kasarmu. Saboda tsibiran Solomon kasa ce mai tasowa, wadda ke da masana’antu kanana da matsakaita masu yawa. Suna fata kuma suna bukatar fitar da kayayyakinsu zuwa manyan kasuwanni. A gani na, karatun kasuwanci na kasa da kasa na iya taimakawa wadannan masana’antu, wajen fadada kasuwannin su, da samun damar da ba za a iya samu ta kasuwannin cikin gida kadai ba.”

Kwanan nan, Julie da wasu dalibai 12 na kasa da kasa sun je birnin Jiangmen na lardin Guangdong don gudanar da ayyukan bincike, inda suka ziyarci garin Tangkou da ke birnin Kaiping, da kauyen Jingmei da ke garin Yamen, da gandun dajin kare muhalli na kananan tsuntsaye, da kauyen Chenpi, da dai sauransu, don samun zurfafa fahimtar yadda ake farfado da yankunan karkara, tarihi da al'adu, da sana'ar matasa a wuraren.

Julie ta ce, irin wannan damar na iya taimaka mata wajen kara fahimtar ci gaban kasar Sin ta hanyoyi uku. Har ila yau, tana mayar da hankali kan damar yin karatu da zama a kasar Sin.

“Ya zuwa yanzu, wadanda na fi godewa a lokacin da nake karatu a kasar Sin su ne malamai na. Suna kula da mu sosai, suna ba mu goyon baya, kuma suna ba mu damar da za mu shiga ayyukan da za su taimaka mana wajen neman ci gaban kai ta fuskar sana'a.”

Julie ta ce a yayin da take makarantar sakandare, ta gano cewa akwai Sinawa da yawa da suke zuwa kasar Solomon don gudanar da kasuwanci. Kuma bisa bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ita kanta ma za ta iya samun karin damammaki a nan gaba. Abin da kawai ya kamata ta yi a yanzu, shi ne ta koyi Sinanci da kyau, da kuma karfafa kwarewarta ta neman samun ci gaba.

“A gani na, iya Sinanci wata fasaha ce mai mahimmanci. Tattalin arzikin Asiya yana bunkasa cikin sauri, musamman kasar Sin. Idan mun koyi Sinanci da kyau, za mu iya yin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya tare da kasar Sin yadda ya kamata.”

Kamar yadda Julie ta ce, tun bayan kulla huldar diflomasiyya, dangantakar dake tsakanin Sin da Solomon ta samu bunkasuwa cikin sauri, kuma ta samu sakamako mai kyau, hakan ya amfanar da jama'ar kasashen biyu, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Kasashen biyu na da matukar dacewa a fannin tattalin arziki, kuma suna da babbar damar yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya, kana suna da kyakkyawar makomar samun ci gaba a nan gaba. Don haka, har ila yau Julie tana mayar da hankali sosai game da jerin hadin gwiwar da kasashen biyu suka cimma ba da dadewa ba, tana fatan ganin za a kara samun ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni.

Game da makomarta a nan gaba, Julie ta bayyana cewa,

“A duk lokacin da na yi magana da iyalina, na kan gaya musu yadda nake yin karatu da zama a kasar Sin. Game da nan gaba, ba ni da wani takamaiman shiri tukuna, amma idan na samu dama, har yanzu ina fatan ci gaba da karatu a nan kasar Sin.”