logo

HAUSA

Al’amuran jin kai a Gaza na kara tabarbarewa yayin da ake ta kara yin kira da a tsagaita wuta

2023-11-12 16:59:17 CMG

A yau Lahadi ne Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa sadarwa tsakaninta da babban asibitin Al-Shifa na Gaza ta katse, inda jami’an Falasdinawa suka ce jarirai biyu sun mutu, wasu da dama kuma na cikin hadari bayan da man fetur ya kare a tsaka da kazamin artabu dake gudana a yankin, yayin da halin jin kai a Gaza ke kara tabarbarewa.

Kakaki rundanar sojin Isra’ila Rear Amiral Daniel Hagari ya ce sojojin na Isra’ila za su taimaka wajen kwashe jarirai daga asibitin.

Isra'ila ta ce dole ne likitoci, da marasa lafiya da dubun mutanen da suka fake a asibitocin arewacin Gaza su fice domin tunkarar mayakan Hamas da ta ce sun sanya cibiyoyin bayar da umarni a karkashin asibitoci ko a kewanyensu. Hamas ta musanta wannan ikirarin.

Motoci bakwai ne kawai daga cikin motocin daukar marasa lafiya 18 na kungiyar agaji ta Red Crescent Society (PRCS) ke tafiya, a cewar wata sanarwa daga PRCS a ranar Asabar. Duk da haka, wadannan motocin daukar marasa lafiya da ke ci gaba da aiki suna cikin hadarin "daina aiki gaba daya cikin sa'o'i masu zuwa" saboda karancin man fetur.

Dubban daruruwan masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu ne suka yi tattaki a tsakiyar birnin London a ranar Asabar, wanda shi ne mafi girma a jerin gwanon da aka gudanar a babban birnin kasar Birtaniya na kiran tsagaita wuta a zirin Gaza.

Duk da ci gaba da kiran da kasashen duniya suka yi na tsagaita bude wuta, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Asabar cewa, yakin da Isra'ila ke yi na murkushe mayakan Hamas zai ci gaba kuma "da karfi".

Tsagaita bude wuta za ta yiwu ne kawai idan an sako dukkan mutane 239 da mayakan suka yi garkuwa da su a Gaza, a cewar Netanyahu a wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin. (Yahaya)