Taron hadin gwiwa na kasashen Larabawa da na Musulmi ya yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ ila ke kai wa a zirin Gaza
2023-11-12 16:58:14 CMG
Mahalarta taron koli na hadin gwiwar kasashen Larabawa da kasashen musulmi da Saudiyya ta shirya a jiya Asabar sun yi Allah wadai da “laifuffukan yaki” da Isra’ila ta aikata a zirin Gaza tare da yin watsi da ikirarin da Isra’ila ta yi na cewa matakin da ta dauka kan Falasdinawa na kare kai ne.
Sanarwar karshe da aka fitar bayan taron na yini guda da ya gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya inda aka tattaro shugabannin kasashen musulmi da na Larabawa da dama da kuma kungiyoyin kasa da kasa domin tattauna halin da ake ciki a zirin Gaza, inda aka bukaci da a kawo karshen yakin da kawanyar da Isra’ila ta yi wa Gaza don ba da damar shigar da kayan agaji.
Sanarwar ta kuma yi kira da a dakatar da fitar da makamai zuwa Isra'ila tare da yin kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ta binciki take hakkin Falasdinawa da Isra'ila ta yi a Gaza.
Mahalarta taron sun sha alwashin tallafawa ayyukan agajin jin kai na Masar a Gaza tare da yin tir da yunkurin korar Falasdinawa daga arewaci zuwa kudancin zirin Gaza ko kuma wajen Gaza.
Taron dai ya samu halartar shugabanni da dama da suka hada da Yarima mai jiran gado na Saudiyya kuma firaministan kasar Mohammed bin Salman Al Saud, da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, da shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi, da shugaban kasar Turkiyya Tayyib Erdogan, da shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, da shugaban Syria Bashar al-Assad, da shugaban majalisar rikon kwarya ta Sudan Abdel Fattah Al-Burhan.
Da halartar taron, Raisi ya zama shugaban kasar Iran na farko da ya ziyarci Saudiyya cikin sama da shekaru goma. Ziyarar ta Raisi ta zo ne bayan da Iran da Saudiyya suka rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya a watan Maris domin daidaita dangantakarsu. (Yahaya)