logo

HAUSA

Jami`an `yan sandan Najeriya sun kammala samun horo a kasar Sin a kan dabarun dakile aikata laifukan ta hanyar yanar gizo

2023-11-12 20:23:11 CMG Hausa

Rundunar `yan sandan Najeriya bisa hadin gwiwa da ma`aikatar kula da harkokin tsaron al`umma ta kasar Sin sun kawo karshen horon makonni biyu da aka shiryawa jami`an `yan sanda a kan hanyoyin dakile laifukan da ake aikatawa ta amfani da yanar gizo.

Wata sanarwa dauke da sa hannun jami`in hulda da jama`a na rundunar `yan sandan Najeriya ACP Olumuyiwa Adejobi wadda aka rabawa manema labarai jiya Asabar 11 ga wata a birnin Abuja ta yi bayanin cewa jami`an ‘yan sandan Najeriya 15 ne suka samu horon a kasar Sin.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

ACP Olumuyiwa yace an gudanar da horon ne bisa kulawar cibiyar nazarin harkokin fasahar kimiyya da gudanarwa ta Shanghai, wanda aka fara daga 29 ga watan jiya na oktoba kuma aka kammala jiya asabar 11 ga watan Nuwanba.

Ya ce taron bitar ya biyo bayan ziyarar da sefeto janaral na `yan sandan Najeriya ya kai kasar China ne wani lokaci a baya, inda ya nemi tallafin mahukuntar kasar wajen kara bukasa ilimi da kwarewar `yan sandan Najeriya wajen shawo kan barazanar tsaro da ake fuskanta ta kafofin yanar gizo a Najeriya.

Tawagar jami`an na Najeriya da suka samu horon kamar yadda sanarwar ta bayyana, tana karkashin mataimakin kwamishinan `yan sanda Muhammad Musa Danko ne, inda dukkanninsu suka bayyana gamsuwa bisa horon da suka samu daga kwararru `yan kasar Sin.

Daga bisani jami`in hulda da jama`a na rundunar `yan sandan ta Najeriya ACP Adejobi ya sanar da cewa Sufeton `yan sandan na Najeriya Mr Kayode Egbetokun yana mika godiyar sa ga kasar Sin bisa daukar nauyin shirin bayar da horon da ta yi.”(Garba Abdullahi Bagwai)