Kwamitin sulhun MDD ya kira taron gaggawa kan yanayin da Palastinu da Isra’ila ke ciki
2023-11-11 15:45:45 CMG Hausa
A jiya Jumma’a ne bisa bukatar tawagar hadaddiyar daular Larabawa, kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da wani taro karkashin jagorancin kasar Sin kan halin jin kai a zirin Gaza, inda zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya bayyana cewa, ya dace a tsagaita bude wuta domin tsaron fararen hula, da kare rayukansu, da kuma samar musu da kayayyaki nan da nan ba tare da bata lokaci ba.
A cikin jawabinsa, Zhang Jun ya yi tsokaci cewa, yanayin da zirin Gaza ke ciki, rikicin jin kai ne, haka kuma rikicin dan adama ne, dole ne daukacin al’ummun kasashen duniya su yi magana da babbar murya, domin daidaita mummunan matsalar. Kuma dole ne kwamitin sulhun MDD ya yi watsi da ra’ayin wasu kasashe ya dauki hakikanin matakai domin tabbatar da adalci da kwanciyar hankali.
Zhang Jun ya kara da cewa, muna kira ga bangarori daban daban, musamman ma manyan kasashe a duniya da su yi kokari tare domin tsagaita bude wuta a yankin, kuma kasar Sin na adawa da duk wani matakin sabawa dokokin jin kai na kasa da kasa da aka dauka a zirin Gaza. (Jamila)