logo

HAUSA

Rahoton MDD: Afirka na samun ci gaba a fannin amfani da hidimomin hada hadar kudi kai tsaye ta na’urorin zamani

2023-11-10 10:22:28 CMG Hausa

 

Wani rahoto da hukumar raya tattalin arzikin nahiyar Afirka ta MDD ko UNECA ta fitar, ya yi nuni da cewa, nahiyar na samun ci gaba a fannonin samar da hidimomin hada hadar kudade nan take ta na’urorin zamani, da bukatar ingancin tsarin.

Rahoton na shekara-shekara, wanda shi ne irinsa na biyu da hukumar ta fitar a ranar Laraba, na mayar da hankali ne ga fayyace halin da gamammen tsarin biyan kudade nan take ke gudana a duk shekara a kasashen Afirka, ko SIIPS a takaice.

Rahoton na UNECA, ya kara da cewa, nasarorin da aka samu a wannan fanni, manuniya ce ga irin ci gaba da kasashen Afirka suke samu, game da burinsu na samar da cikakke, kuma gamammen tsarin biyan kudade ko IPS, a matsayin bangaren raya ababen more rayuwar al’ummar Afirka ta fuskar fasahohin sadarwa, da kago kyakkyawan tsarin raya tattalin arziki, da bunkasa kasuwanci da jagoranci na dijital.

Bugu da kari, rahoton ya ce, sabbin tsare-tsaren biyan kudade 3 da aka kaddamar a kasashen Habasha, da Morocco, da Afirka ta kudu cikin watanni 12 da suka gabata, sun kara yawan adadin wadanda ake da su a sassan nahiyar zuwa 32.

Har ila yau, rahoton ya ce jimillar hada-hadar biyan kudade, da wadanda ake aiwatarwa sun karu cikin sauri tun daga shekarar 2018, da kaso 47 da 39. A daya bangaren kuma, a shekarar 2022 da ta gabata, gamammen tsarin biyan kudade ko IPS a kasashen na Afirka, ya ingiza nasarar hada-hada kusan biliyan 32, wadda darajarta ta kai kusan dala tiriliyan 1.2.   (Saminu Alhassan)