logo

HAUSA

Isra’ila ta ce an dakatar da kai farmaki na dan lokaci a wasu wurare dake Gaza a maimakon tsagaita wuta baki daya

2023-11-10 11:43:10 CMG Hausa

Rundunar sojojin Isra’ila ta sanar da dakatar da kai hare-hare a wasu sassa na Gaza na wani dan lokaci bisa tsare-tsare, don bayar da damar samar da tallafin jin kai ga fararen hula, matakin da yake da wa’adi, da kuma wurare kebantattu.

Sanarwar ta ce, bangaren Isra’ila ya samar wa fararen hula dake Gaza damar kaura zuwa yankunan kudu masu tsaro, ta yadda za su sami tallafi.

A wata sanarwar da sojojin tsaron Isra’ila suka bayar a jiya Alhamis kuma, sun ce tun bayan barkewar rikicin Falasdinu da Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, an harba makaman roka kusan 9500 kan yankunan Isra'ila, kuma yawancinsu daga Gaza.

Hukumomin kiwon lafiya a Gaza, sun sanar a jiya Alhamis cewa, tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, ayyukan soja da sojojin Isra’ila suka aiwatar a Gaza, sun riga sun haddasa mutuwar Falasdinawa 10,790. Kaza lika bisa kididdigar da gwamnatin Isra’ila ta fitar, rikicin na wannan karo ya haddasa mutuwar mutane 1400 a bangaren Isra’ila, baya ga wasu 240 da ake tsare da su a Gaza. (Safiyah Ma)