logo

HAUSA

Hukumar kwastam a Najeriya ta fara daukar matakai na rage cunkoson kaya a tasoshin ruwan kasar

2023-11-10 09:10:29 CMG Hausa

 

Hukumar lura da shige da ficen kayayyaki a tarayyar Najeriya Kwastam ta kaddamar da kwamitin da zai lura da yadda za a magance matsalolin cunkoso a tasoshin ruwan kasar ta hanyar gwanjon wasu kayayyaki da suka shafe shekaru ba tare da an dauke su ba.

A lokacin da yake kaddamar da kwamitin a hedikwatar hukumar dake birnin Abuja, shugaban hukumar Bashir Adewale Adeniyi ya ce, ci gaba da karuwar kwantainonin ’yan kasuwa a tasoshin yana matukar shafar gudanuwar harkokin kasuwanci na kasa da kasa a Najeriya wanda wannan barazana ne ga ci gaban tattalin arziki.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

’Yan kwamitin sun kunshi wakilai daga ma’aikatar shari’a kasar da ma’aikatar kudi da ta lura da tasoshin ruwa da kuma wakilcin hukumomin tsaron kasar da suka hada da hukumar ’yan sanda da ta tsaro na DSS.

Shugaban hukumar kwastam din ya kara da cewa, yana daga cikin aikin kwamiti fito da mataki na karshe da zai warware jinkiri na tantance kayayyakin da ake shigowa da su Najeriya ta tasoshin ruwan.

Malam Abdullahi Maiwada shi ne babban jami’in yada labaran hukumar kwastam na tarayyar Najeriya.

“Shekaru da dama mun samu tsaiko na irin wadannan kaya, wadansu sun yi shekara da shekaru a wannan wurin, shi ne aka bayar da umarnin cewa a yi yadda za a yi a bi tsari na doka wajen fitar da wadannan kayayyaki daga tasoshin, kuma akwai sabuwar doka ta hukumar kwastam wato Nigeria Custom Service Act 2023, dokar ta bayar da dama kan yadda za a yi a fitar da wadannan kaya da yadda kuma za a yi gwanjonsu, kwamitin zai yi aiki ne bisa jagorancin wannan doka, ba za a iya cewa ga wa’adin da za su kammala aikin nasu ba saboda kwantainonin suna da yawa, amma dai za a yi aikin cikin sauri domin cimma burin ganin cewa kasuwanci ya habaka a iyakokinmu na ruwa, wanda suke son fitar da kayansu sun fitar wanda kuma suke son shigo da kayansu sun shigo.”

Karkashin wannan doka, kayan da suke karkashin kulawar kotu ne kawai hukumar ta kwastam ba za ta fitar da su ba daga tasoshin ruwan. (Garba Abdullahi Bagwai)