Kasar Sin na adawa da duk wani abu da zai yi illa ga fararen hula da keta dokokin kasa da kasa
2023-11-10 11:33:19 CMG
Kasar Sin ta ce tana adawa tare da tir da duk wani abu da ka iya kawo illa ga fararen hula da take dokokin jin kai na kasa da kasa.
Manzon musamman na kasar Sin kan batun Gabas ta Tsakiya Zhai Jun ne ya bayyana haka a jiya Alhamis, yayin wani taron jin kai na kasa da kasa kan tallafawa fararen hula a Gaza, da ya hallara shugabannin kasashen duniya da jami’ai daga hukumomin kasa da kasa.
A cewar manzon na kasar Sin, kasarsa ta damu matuka da sabon zagayen rikicin Palasdinu da Isra’ila da ya kwashe sama da wata guda ana yi, lamarin da ya yi sanadin rayukan fararen hula da dama tare da tabarbarewar yanayin jin kai.
Ya ce kasar Sin na goyon bayan duk wani yunkuri na rage rikicin da komawa teburin tattaunawar zaman lafiya, haka kuma tana maraba da duk wata shawarar da za ta dace da kare fararen hula da saukaka matsalar jin kai.
Zhai Jun ya kara da cewa, kasar Sin ta kasance mai inganta tattaunawar zaman lafiya, kuma tana goyon bayan muradin Palasdinawa na dawo da halaltattun hakkokinsu. Haka kuma, tana fatan ganin wanzuwar zaman lafiya tsakanin Palasdinu da Isra’ila. (Fa’iza Msutapha)