logo

HAUSA

Ma’aikatar ayyukan jin kai a Najeriya za ta hada kai da hukumar kidayar jama’a wajen bayar da tallafi ga ’yan kasa

2023-11-09 09:23:37 CMG Hausa

Ma’aikatar lura da ayyukan jin kai da yaki da talauci a tarayyar Najeriya ta bukaci hukumar kidayar jama’a ta kasar da ta samar mata da cikakkun bayanan ’yan kasa domin amfani da shi a tsare-tsarenta na bayar da tallafin rayuwa ga ’yan kasar.

Ministar ma’aikatar Mrs Betta Edu ce ta bukaci hakan a birnin Abuja yayin wani taro da shugabannin hukumar kidaya ta kasa karkashin jagorancin shugaban hukumar Malam Nasir Kwarra.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mrs. Betta Edu ta ce, samu kudin bayanan ’yan Najeriya daga hukumar kidayar zai taimakawa ma’aikatar tata matuka wajen cimma manufofin gwamnati mai ci na fitar da miliyoyin ’yan Najeriya daga kangin talauci. 

Ministar ta ce, ba kowa ne yake cikin halin talauci ba a Najeriya, a saboda haka wajibi ne a tantance domin tabbatar da ganin tagomashin ya isa ga ainihin mutanen da gwamnati ta yi hasashen agazawa.

“Hukumar tana da ma’aikata a yankunan kananan hukumomi, saboda haka wadannan ma’aikata su ne za mu yi aiki da su, za mu samar da kwamitin da ya kunshi ma’aikatan hukumar kidayar ta kasa da kuma na ma’aikatar jin kai wanda kwamitin ne kuma zai fito da irin gudummawar da kowanne bangare zai bayar, hakan zai samar da cikakken tsarin da za a bi wajen aiwatar da shirin yaki da talauci a kasa baki daya.”

A jawabinsa shugaban hukumar kidayar jama’a a tarayyar Najeriya Malam Nasir Kwarra ya yi alkawarin cewa hukumar tasa za ta bayar da dukkannin hadin kan da ya kamata a kokarin da ma’aikatar ayyukan jin kai ke yi na bayar da tallafin rayuwa ga ’yan Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)