logo

HAUSA

An bude dandalin zuba jari na Afirka na 2023 a Morocco

2023-11-09 12:20:51 CMG Hausa

A jiya Laraba ne aka fara taron Ranakun Kasuwanci na Dandalin Zuba Jari na Afirka (AIF) na 2023 a birnin Marrakech na kasar Morocco. 

Taron wanda aka gudanar a karkashin taken “Habaka hada-hadar kasuwancin Afirka” an bude shi ne da jawabin Sarkin Morocco Mohammed VI. Taron na kwanaki uku, ya samu manyan mahalarta kusan 600, da suka hada da shugabannin kasashe, masu yanke shawara, manyan kamfanonin duniya da masu zuba jari, da nufin samar da muhimmiyar hadin gwiwa don samar wa masu zuba jari damammaki a wannan zamanin da ake sauye-sauye ga nahiyar. (Muhammed Yahaya)