logo

HAUSA

Wakilan Sin da na Amurka sun kammala tattaunawa game da sauyin yanayi

2023-11-09 16:04:34 CMG Hausa

Wata sanarwar da ma’aikatar kula da muhalli da muhallin halittu ta kasar Sin ta fitar a Alhamis din nan, ta ce an cimma nasarori yayin taron sauyin yanayi da ya gudana a jihar California ta Amurka tsakanin wakilan Sin da na Amurka.

An kammala tattaunawar ne dai a jiya Laraba, bisa jagorancin wakilin musamman na kasar Sin game da sauyin yanayi Xie Zhenhua, da wakilin musamman na shugaban kasar Amurka kan sauyin yanayi John Kerry.  (Saminu Alhassan)