logo

HAUSA

An gudanar da taron karawa juna sani kan tsaro da raya dangantakar Sin da Afirka a Zimbabwe

2023-11-09 18:55:40 CMG Hausa

A jiya ne, aka gudanar da taron karawa juna sani kan yanayin tsaro a Afirka, da raya dangantakar tsakanin kasasen Sin da Afirka, taron da ya samu halartar jami'an ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Zimbabwe da masana daga fannonin zaman lafiya, da tsaro, da bunkasuwa da ma tarihi a kasar.

Babban sakataren kungiyar tabbatar da zaman lafiya da kwance damara ta jama'ar kasar Sin (CPAPD), daya daga wadanda suka dauki nauyin shirya taron, An Yuejun, ya bayyana a yayin muhimmin jawabin da ya gabatar cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka a fannin tsaro, yana daya daga cikin muhimman al'amurran hadin gwiwa da aka bayyana karara a manufar daftarin aiki na shawarar samar da tsaro a duniya.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana son ba da gudummawar hadin gwiwa wajen aiwatar da shawarar samar da tsaro na duniya tare, da gina al'ummar Sin da Afirka mai makoma guda, da kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka. (Ibrahim)