logo

HAUSA

Wadanne damammaki da aka samu cikin abubuwan da aka nuna a karon farko a duniya a CIIE?

2023-11-09 12:36:32 CMG Hausa

A yayin bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin CIIE karo na shida da ake gudanarwa a birnin Shanghai, an baje sabbin kayayyaki masu dimbin yawa, kamar abin tsaftace kujerun zama a falo, da labulaye ba tare da cire su daga muhallin su ba, da na’urar zamani ta yin kwalliyar fuska, wadanda suke kunshe da manyan fasahohi kamar basirar dijital, da fasahohi marasa gurbata muhalli.