logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin ya bukaci kotun ICC da ta kaucewa nuna banbanci da wariya

2023-11-09 10:05:20 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Zhang Jun, a jiya Laraba ya bayyana fatan cewa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) za ta kaucewa nuna banbanci da wariya

Zhang ya shaidawa taron kwamitin sulhu na MDD game da kasar Libya cewa, kasar Sin tana goyon bayan tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, ta hanyar yin la’akari da manyan laifukan kasa da kasa. 

Zhang ya ce, a bayyane matsayin kasar Sin yake, dangane da ayyukan kotun ICC a kasar Libya, "Dole ne mu bi ka'idar da Libya ta gindaya, mu mutunta ra'ayin al'ummar Libya, da kuma kaucewa mafitar da za a dorawa kasar daga waje." Zhang ya kuma kara da cewa, kamata ya yi aikin da kotun ta ICC za ta yi ya taimaka wajen inganta tsarin siyasa da zaman lafiya a kasar Libya, da taimaka wa bangarorin kasar su karfafa hadin kai, da samar da daidaito, tare da kaucewa kara ingiza sabanin ra'ayi. (Muhammed Yahaya)