logo

HAUSA

Sin Na Taka Rawar Gani Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya

2023-11-09 18:33:33 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

Tun bayan barkewar sabon zagayen tashin hankali tsakanin Falasdinawa da dakarun Isra’ila, mutane sama da 11,000 sun rasa rayukansu a Gaza, wanda hakan ya yi matukar tada hankalin sassan kasa da kasa, kuma tuni kasashen duniya suka fara kiraye-kirayen ganin an gaggauta dakatar da bude wuta, tare da kawo karshen zubar da jini.

A bangaren sassa dake taka rawar gani wajen ganin an kawo karshen wannan tashin hankali, ko shakka babu kasar Sin ta yi fice, ganin yadda tun farkon lamarin mahukuntan take ta tattaunawa da sassan masu ruwa da tsaki, kaza lika Sin ta yi tsayin daka wajen tattaunawa da ragowar kasashen duniya karkashin kwamitin tsaron MDD, kana ta yi duk mai yiwuwa wajen ingiza dawo da zaman lafiya, da kai zuciya nesa, domin ganin an yayyafawa wutar tashin hankalin ruwa.

Bisa himma da kasar Sin ke yi, da mayar da hankali sosai kan wannan lamari, ta lura da manyan bukatun da ake da su na shawo kan lamarin, har ma ta gabatar da matsaya karkashin jigo 4.

Da farko dai kasar Sin na tsaye kan burin tabbatar da an kare mutuntaka, wato aiwatar da dukkanin matakai na kare hakkokin dan Adam na rayuwa, kamar dai yadda dokokin jin kai na kasa da kasa suka tanada. Na biyu kuwa, Sin ta yi amanar cewa, aiwatar da matakan siyasa ne kadai za su ba da damar kawo karshen yakin da ake gwabzawa tsakanin Falasdinawa da tsagin Isra’ila. Sai kuma na uku, wato cudanyar sassa daban daban, ta fannin shawarwari da aiwatar da matakan da suka dace, wanda zai taimaka matuka wajen ganin bayan wannan rikici. Sannan kuma na hudu, Sin ta yi imanin cewa, wajibi ne a magance tushe, da kuma abubuwan da suka haifar da wannan rikici wanda ke ta maimaituwa tsawon lokaci. Karkashin hakan, kasar Sin na ganin dole ne a tabbatar da kafuwar kasashe biyu masu cin gashin kansu, matakin da zai tabbatar da cikakken ’yancin Falasdinawa na samun kasarsu.

Idan mun yi la’akari na wadannan batutuwa da Sin ke tsaye a kansu, tabbas za mu gamsu da kyakkyawar manufar kasar, ta ganin an kawo karshen zubar jini tsakanin wadannan sassa biyu, da ma cimma burin ganin an bunkasa zaman lafiya da jituwa a gabas ta tsakiya. (Saminu Alhassan)