logo

HAUSA

Kasar Sin za ta inganta kirkire-kirkire da bude kofa da gabatar da karin damarmaki ga duniya

2023-11-09 12:19:22 CMG Hausa

Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da inganta kirkire-kirkire da ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya da kara hadin gwiwa ta hanyar bude kofarta da kuma gabatar da karin damarmakin zuba jari da kasuwa ga sauran sassan duniya.

Han Zheng ya bayyana haka ne cikin jawabin da ya gabatar ga taro kan sabon tsarin tattalin arziki na Bloomberg a Singapore.

A cewarsa, Sin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kara bude kofa ga duniya, kuma a shirye take ta samar da karin damarmakin zuba jari da kasuwa domin kamfanonin kasashen waje su ci gajiyar bude kofarta.

Ya kara da cewa, Sin za ta kara matsa kaimi wajen yayata nasarorin da ta samu a fannin kirkire-kirkire ga sauran kasashe, da hada hannu da su wajen magance kalubalen sauyin yanayi da kara sabon kuzari ga ci gaban tattalin arzikin duniya. (Fa’iza Mustapha)