Sin da Rasha za su kare zaman lafiya da ci gaban duniya
2023-11-09 10:06:50 CMG Hausa
Mataimakin shugaban hukumar soja ta kwamitin kolin JKS janar Zhang Youxia, ya ce a shirye kasar Sin take ta hada hannu da Rasha, domin kare muradun kasashen biyu da kare zama lafiya da ci gaban duniya.
Janar Zhang Youxia ya bayyana haka ne jiya, lokacin da yake ganawa da shugaban Rasha, Vladimir Putin a Moscow.
Yayin ganawar, Vladimr Putin ya ce dangantakar abota dake tsakanin Rasha da Sin, ta dace wajen wanzar da zaman lafiyar yankinsu da ma duniya. Yana mai cewa dangantakar ta bambanta da wadda aka gani a lokacin yakin cacar baka..
A nasa bangare, janar Zhang Youxia, ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da Rasha wajen aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin rundunonin sojin kasashen biyu da kare muradunsu da kare zaman lafiya da ci gaban duniya da ma yankunansu. (Fa’iza Mustapha)