logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a dakatar da bude wuta a rikicin Isra’ila da Falasdinawa

2023-11-08 10:11:43 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce kasar na kira da a gaggauta dakatar da bude wuta a rikicin da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Geng ya ce tun bayan barkewar sabon zagaye na dauki ba dadi tsakanin sassan biyu, Falasdinawa a Gaza sun tsunduma cikin mummunan yanayi na hare-haren bama-bamai. Jami’in ya hakaito kalaman babban magatakardar MDD Antonio Guterres, wanda ya ce “A halin da ake ciki al’ummar Gaza na fuskantar mafi munin yanayin rayuwa.”

Geng Shuang, wanda ya yi tsokacin yayin zaman taron kwamitin na 4 na taron MDD game da matakan da Isra’ila ke aiwatarwa, da batun matsugunnai da yankunan da aka mamaye, ya sake jaddada cewa, ya zama wajibi a yi tir da duk wasu matakai na kaiwa fararen hula farmaki, kana a yi watsi da duk wani mataki na keta dokokin kasa da kasa. 

Ya ce ba za a taba amincewa da amfani da karfin tuwo ba. Bai kuma dace a rika kaddamar da hare-hare kan ababen more rayuwar jama’a, kamar asibitoci, da makarantu, da sansanonin ’yan gudun hijira ba.

Daga nan sai Geng ya gabatar da kiran kasar Sin ga dukkanin sassa masu ruwa da tsaki a wannan rikici, da su amsa bukatar sassan kasa da kasa na gaggauta tsagaita wuta, da kawo karshen tashin hankali, da dakatar da musayar wuta, da daukar duk wasu matakai na dakile sake ta’azzar al’amura. (Saminu Alhassan)