logo

HAUSA

Burin Sin Na Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya Bai Sauya Ba

2023-11-08 19:11:43 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

Yanzu haka dai hankalin duniya ya karkata ne ga rikicin dake faruwa tsakanin Palasdinu da Isra’ila, inda duk wayewar gari rayuka ke salwanta tsakanin bangarorin biyu.

Kuma tun kafin ta zama shugabar karba-karba ta kwamitin sulhun MDD, kasar Sin ke ta kira tare da gabatar da matakai a lokuta daban-daban, na kawo karshen tashe-tashen hankulan dake faruwa a sassan duniya. Sannan bayan da ta karbi shugabancin karba-karba na kwamitin sulhun MDD, kasar Sin ta jaddada kudurinta na ci gaba da yin hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa, wajen sa kaimi ga kwamitin sulhu na MDD na daukar matakan da suka dace na tsagaita bude wuta, da kawo karshen yaki, da rage yanayin jin kai da ake ciki, da taka rawar da ta dace wajen samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Falasdinu da Isra'ila ta hanyar "shirin kafa kasashe biyu".

Sin na kara bayyana cewa, wajibi ne kasashen duniya su dauki matakin gaggawa, kuma kasashen dake wajen yankin, musamman ma manyan kasashe, su tabbatar da gaskiya da adalci, tare da taka rawa mai ma'ana wajen ganin an sassauta yanayin da ake ciki.

Idan ba a manta a ranar 1 ga watan Nuwamba, lokacin da kasar Sin ta karbi wannan shugabanci, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya bayyana cewa, halin da ake ciki tsakanin Falasdinu da Isra’ila shi ne batu mafi muhimmanci a ajandar kwamitin sulhu na wannan wata. Kana aikin dake kan gaba shi ne karfafa maganar tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin, da hana karin asarar rayukan fararen hula, bala'un jin kai, da rikice-rikice.

Kamar kullum Sin na Allah wadai da duk wasu matakai na muzgunawa, da kaiwa fararen hula hare-hare, domin rayukan al’umma na da matukar alfarma, kuma bai dace tashin hankalin da ake fama da shi ya haifar da salwantar rayukan fararen hula Falasdinawa ko Isra’ilawa ba.

Sin mai kaunar zaman lafiya na kira da a gaggauta komawa teburin shawarwari, domin kaiwa ga cimma matsaya, dangane da aiwatar da manufar nan ta warware riciki ta hanyar kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, a kuma shata matakai daki-daki na cimma nasarar hakan.

Kuma a matsayinta na shugabar kwamitin sulhu na majalisar na wannan karo, kasar Sin za ta yi biyayya ga kiraye-kirayen kasashen duniya, da yin aiki tare da bangarorin da abin ya shafa, wajen sa kaimi ga kwamitin don daukar matakai na bai daya masu ma'ana cikin lokaci.

Wannan ya kara nunawa duniya cewa, kasar Sin tun fil-azal, kasa ce mai kaunar zaman lafiya ba neman tashin hankali ba. Sabanin wasu kasashe dake amfani da matsayi ko ikonsu na kara rura wutar fitina, ba tare da la’akari da rayukan dake salwanta ba. Domin zaman lafiya ya fi zama dan Sarki. (Ibrahim Yaya)