logo

HAUSA

Li Qiang ya aike da sakon taya murna ga sabon firaministan kasar Kwadifwa

2023-11-08 10:48:00 CMG Hausa

A ranar 7 ga watan Nuwamba ne firaministan kasar Sin Li Qiang ya aike da sakon taya murna ga firaministan kasar Kwadifwa Robert Beugré Mambé bisa nadin da aka yi masa a matsayin firaminstan kasar Kwadifwa. 

Li Qiang ya ce, Sin da Kwadifwa aminan juna ne kuma abokan hulda. A bana ne aka cika shekaru 40 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. A halin yanzu, dangantakar dake tsakanin Sin da Kwadifwa tana samun ci gaba mai inganci, amincewar juna ta fuskar siyasa tana karuwa, kuma ingantaccen hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya” tsakanin bangarorin biyu na samar da kyakkyawan sakamako.

Li ya kara da cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Kwadifwa, kuma a shirye yake ya yi aiki da Mambé wajen aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da sa kaimi ga samun sabbin nasarori a hadin gwiwar abokantaka tsakanin kasashen biyu. (Yahaya)