logo

HAUSA

AU ta bayyana matukar damuwa game da ci gaba da samar da kudi ga ‘yan ta’adda a Afrika

2023-11-08 09:49:46 CMG Hausa

 

Kungiyar Tarayyar Afrika AU, ta bayyana matukar damuwa game da yadda ake ci gaba da samar da kudi ga ayyukan ta’addanci a Afrika.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamitin tsaro da wanzar da zaman lafiya na AU ya fitar bayan taronsa a jiya, game da yaki da ta’addanci a nahiyar.

A cewar sanarwar, kwamitin ya damu matuka da yadda ake ci gaba da samar da kudin gudanar da ayyukan ta’addanci, musammam karuwar alaka tsakanin ta’addanci da laifuffukan da ake aikatawa tsakanin kasa da kasa, ciki har da safarar miyagun kwayoyi da cinikayyar albarkatu da hada-hadar kudi ta harmatacciyar hanya, wadanda ke mummunan tasiri kan tattalin arzikin kasashen kungiyar.

Ta kara da cewa, barazanar da tsaro da zaman lafiya ke fuskanta a Afrika na haifar da koma-baya ga ci gaban da aka samu wajen cimma burikan ci gaban Afrika na Ajandar shekarar 2063 da muradun ci gaba masu dorewa na MDD.

Kwamitin ya kuma yi kira ga kasashe mambobin AU su kauracewa ingizawa da kitsawa da shiryawa har ma da shiga harkokin samar da kudi ko karfafa ayyukan ta’addanci. (Fa’iza Mustapha)