Yadda Sin da sauran kasashe ke kara yin hadin gwiwar kimiya da fasaha karkashin BRI
2023-11-08 11:03:16 CMG Hausa
A wannan makon ne aka bude taron shawarar “ziri daya da hanya daya” kan musayar kimiyya da fasaha na farko a birnin Chongqing dake yankin kudu maso yammacin kasar Sin.
A cikin wasikar taya murna da ya aikewa taron, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, an yi nasarar gudanar da dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na uku a birnin Beijing, wanda ya haifar da wani sabon mataki na ci gaba mai inganci ga shawarar “ziri daya da hanya daya”, kuma hadin gwiwar kimiyya da fasaha wani muhimmin bangare ne daga ciki.
Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga ruhin hanyar siliki bisa zaman lafiya da hadin gwiwa, tare da gaskiya da fahimtar juna, da samun moriyar juna, da aiwatar da cikakken shirin hadin gwiwa na kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, da sa kaimi ga yin mu'amalar kirkire-kirkire na kasa da kasa, kuma a shirye kasar Sin take ta yi hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen samar da damar samun bunkasuwar kirkire-kirkire, da ba da damar yin hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire, a dukkan fannoni don amfanar da jama'a daga dukkan kasashen duniya, ta yadda za su ba da gudummawa mai inganci ga ci gaban shawarar “ziri daya da hanya daya” da gina al'umma mai makomar bai daya ga bil'adama.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne, kamfanin sadarwa na kasar Sin wato Huawei, ya yi hadin gwiwa da takwarorinsu na kasar Kenya wajen samar da wayoyin salula masu inganci da araha, baya ga irin wadannan hadin gwiwa da kasar ta kulla da Najeriya a fannin harba tauraron dan-Adam na sadarwa, da kafa fasahohin aikin gona a wasu kasashen Afirka da sauransu.
Wadannan kadan ne daga cikin sassan da Sin ke yin hadin gwiwa da sauran kasashe musamman kasashe masu tasowa a fannin kimiyya da fasaha karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)