Manzon musamman Sin kan batun yankin Gabas ta tsakiya zai halarci taron tallafin jin kai a Gaza
2023-11-08 19:12:26 CMG HAUSA
DAGA CMG HAUSA
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin ya shedawa manema labarai a yau Laraba cewa, manzon musamman gwamnatin Sin kan batun yankin Gabas ta tsakiya Zhai Jun, zai halarci taron jin kai na kasa da kasa na tallafawa fararen hula na Gaza a kasar Faransa da za a gudanar gobe. Kasar Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya, wajen sa kaimi ga tsagaita bude wuta, da kawo karshen yakin nan da nan, da kare fararen hula, da ba da agajin jin kai, da aiwatar shirin kafa kasashe biyu.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasashen Larabawa da na Musulunci wajen hada kai da kara yin kokari na shiga tsakani don sa kaimi ga tsagaita bude wuta da yaki, da maido da shawarwarin zaman lafiya. Haka kuma, Sin ta yi kira ga bangarorin da abin da ya shafa da su kira wani taron kasa da kasa a hukumance, don cimma matsaya daya kan farfado da tabbatar da manufar kafa kasashe biyu.
Game da ziyarar da firaministan kasar Ausrtiliya ya kawo Sin a kwanakin nan, Wang Wenbin ya ce, yayin ziyararsa, shugabannin kasashen biyu sun tattauna kan batutuwa dake shafar bangarori daban-daban tare da samun ci gaba mai armashi. Sin na fatan hada kai da Austriliya don kara karfafa shawarwari da hadin gwiwa, da zurfafa amincewa da juna a siyasance da samar da karin moriya ga kasashen biyu da jama'arsu. (Amina Xu)