logo

HAUSA

Nuraddeen Ibrahim Adam: Malamin dake himmatuwa wajen koyar da yaren Hausa a kasar Sin

2023-11-07 15:20:19 CMG Hausa

Nuraddeen Ibrahim Adam, tsohon mai sauraron shirye-shiryen sashin Hausa na gidan rediyon kasar Sin ne, wanda a yanzu haka yake koyar da harshen Hausa a jami’ar koyon harsunan waje ta Tianjin wato TFSU dake arewacin kasar Sin.

Kawo yanzu, malam Nuraddeen ya riga ya shafe tsawon shekaru kusan biyar yana koyar da harshen Hausa a jami’ar TFSU, amma sakamakon bullar cutar numfashi ta COVID-19, ya yi wasu shekaru yana koyarwa ta yanar gizo ta Intanet daga birnin Kano. Ga shi yanzu ya sake samun damar dawowa birnin Tianjin, don koya wa daliban kasar Sin harshen Hausa fuska da fuska.

A zantawarsa da Murtala Zhang kwanan baya, malam Nuraddeen ya bayyana dabaru, da hanyar da ake bi wajen koyar da harshen Hausa, da kuma burin da yake kokarin cimmawa. Haka kuma ya yaba da wasu sabbin hanyoyin da sashin Hausa na rediyon kasar Sin ke amfani da su a ‘yan shekarun nan don gabatar da shirye-shirye. (Murtala Zhang)