Geng Shuang: Ya zama wajibi a kaucewa ketara iyakar dokokin jin kai
2023-11-07 10:24:47 CMG Hausa
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya jaddada muhimmancin kaucewa ketara iyakar dokokin jin kai na kasa da kasa a rikicin Isra’ila da Falasdinawa.
Geng ya yi wannan kira ne yayin zaman kwamiti na 4, na babban taron MDD na jiya Litinin, wanda ya yi nazari game da ayyukan tallafi da MDD ke samarwa ’yan gudun hijirar Falasdinawa a gabas maras nisa ko UNRWA a takaice.
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin na Allah wadai da duk wasu matakai na muzgunawa, da kaiwa fararen hula hare-hare. Ya ce rayukan al’umma na da matukar alfarma, kuma bai dace tashin hankalin da ake fama da shi ya haifar da salwantar rayukan fararen hula Falasdinawa ko Isra’ilawa ba.
Mista Geng ya ce Sin na kira da a gaggauta komawa teburin shawarwari, domin kaiwa ga cimma matsaya, don gane da aiwatar da manufar nan ta warware riciki ta hanyar kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, a kuma shata matakai daki-daki na cimma nasarar hakan. A cewarsa, Sin za ta yi aiki tare da sassan kasa da kasa wajen gaggauta kawo karshen yaki a zirin Gaza, da saukaka matsanancin halin jin kai, da samar da jituwa tsakanin Falasdinawa da al’ummar Isra’ila, da ma cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin gabas ta tsakiya.
A wani ci gaban kuma, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya shaidawa taron manema larabai a jiya Litinin cewa, mummunan tashin hankali dake wakana a Gaza, ya haifar da matukar bukatar gaggauta samar da tallafi. Ya ce halin da ake ciki a Gaza, ya wuce bukatun jin kai kadai, domin yanayin ya kai ga zama mummunan bala’i ga bil Adama.
A daya bangaren kuma, wani babban jami’in kasar Afirka ta kudu, ya ce majalissar zartaswar kasarsa ta yanke shawarar yiwa jakadunta dake Isra’ila kiranye, da nufin jin ta bakin su game da halin da ake ciki a Gaza. (Saminu Alhassan)