Abarbar Benin ta shaida yadda kasar Sin ke ta kara bude kofarta
2023-11-07 21:49:18 CMG Hausa
Daga Lubabatu Lei
Wani abokina ya taba zuwa kasar Benin a wasu shekaru da suka wuce, bayan da ya koma gida, ya kan tuna da irin abarba mai dadin gaske da ake samarwa a kasar ta Benin.
A kwanakin da suka wuce, wannan abokina ya yi matukar farin ciki da gaya min cewa, an amince da shigowa da abarba na ake samarwa a Benin kasuwar kasar Sin, don haka ma zai samu damar dandana su a gida ba tare da yin doguwar tafiya har zuwa Benin ba.
Abarba na daga cikin muhimman nau’o’in amfanin gona da ake samarwa a kasar Benin, wanda ake mata kirarin “Burodi mai zaki na Afirka”, sakamakon irin da dandanonta na musamman. A yayin da shugaban kasar Benin ya kawo ziyara kasar Sin a watan Satumban bana, kasashen biyu sun daddale yarjejeniya game da shigowa da danyen abarba na Benin kasuwar kasar Sin.
Watanni biyu ne kacal, sai an fara ganin abarba na Benin a gun bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin(CIIE) karo na shida da yanzu haka ke gudana a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, wadda ta yi matukar janyo hankalin al’umma. A game da wannan, jakadan kasar Benin a kasar Sin, Simon Pierre Adovelande ya bayyana cewa, “ina fatan masu sayayya na kasar Sin za su samu damar fahimtar abarba mai dadi na Benin, kuma muna fatan samu ‘yan kasuwar kasar Sin da za su kai abarbarmu a kasuwar kasar, har ma da teburin al’ummar Sinawa.”
A cikin ‘yan shekarun baya, kasar Sin ta yi ta sa kaimin shigowa da kayayyaki masu inganci na kasa da kasa, don duniya ta more babbar kasuwarta da ma moriyar ci gabanta. Abin lura shi ne, kasar Sin ta kafa kafar musamman ta shigowa da amfanin gona na kasashen Afirka, don tallafawa kasashen Afirka wajen fitar da karin amfanin gonarsu. Da Avokado na Kenya da barkono na Ruwanda da Lemo na Afirka ta Kudu da wake na Tanzania, har da Abarba na Benin, karin kayayyakin kasashen Afirka na samun damar shigowa babbar kasuwar kasar Sin, wadanda a sa’i daya suka kyautata rayuwar al’ummar Sinawa, a sa’i dayan kuma, suka taimaka ga ci gaban tattalin arzikin kasashen da ke fitar da kayayyakin.
Bana ta cika shekaru 45 da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, da shekaru 10 da Sin din ta gabatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, haka kuma ta kasance shekara ta shida da kasar ta shirya bikin baje kolin kayayyaki da ake shigowa da su kasar Sin, bikin da ya kasance irinsa na farko a duniya da ke mai da hankali musamman a kan kayayyakin da ake shigarwa daga ketare. A yayin da farfadowar kariyar ciniki da ra’ayin cacar baka ke haifar da barazana ga dunkulewar tattalin arzikin duniya, yadda kasar Sin ke tsayawa tsayin daka a kan bude kofarta ga ketare, da ma kawar da shingen ciniki tare da kasashen da suka karbi shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, ya shaida niyyarta wajen ganin an tabbatar da ci gaban bai daya na kasa da kasa, haka kuma ya bayyana ma’anar “Gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adam” da ta gabatar.(Mai Zane:Mustapha Bulama)