logo

HAUSA

Shugaban Uganda ya soki Amurka dangane da cire kasarsa daga yarjejeniyar kasuwanci

2023-11-07 10:32:00 CMG Hausa

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya soki Amurka bisa matakin da ta dauka a baya-bayan nan na cire kasarsa daga wata yarjejeniyar kasuwanci tare da yin gargadi game da hadarin yin kasuwanci a kasar ta gabashin Afrika.

Bayan kasar ta zartar da dokar yaki da auren jinsi, Washington ta zargi gwamnatin Uganda da take hakkokin bil adama. Kuma sai a makon da ya gabata, Amurka ta sanar da cire Uganda da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Gabon da Niger, daga cikin yarjejeniyarta ta kasuwanci da kasashen Afrika da ake kira AGOA. Yarjejeniyar AGOA na ba kayayyakin kasashen yankin kudu da Hamadar Sahara damar shiga Amurka ba tare da biyan haraji ba. (Fa’iza Mustapha)