logo

HAUSA

AGOA: Tallafi ko Makami?

2023-11-07 19:26:12 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

A farkon wannan mako ne, shugaban Uganda Yoweri Museveni, ya soki matakin Amurka na cire kasarsa daga yarjejeniyar cinikayya ta AGOA, saboda abun da Amurka ta kira “take hakkokin bil adama”.

AGOA, yarjejeniya ce da Amurka ta gabatar a shekarar 2000 domin ba kasashen kudu da hamadar Sahara damar shigar da wasu kayayyaki sama da 1,800 cikin Amurkar ba tare da biyan haraji ba.

Sai dai, matakin Amurka ya sa alamar tambaya kan me taimakonta ke nufi: tallafi domin ci gaban kasashe ko kuma makamin tilasta musu akidunta? Matakin Amurka ya bayyana karara yadda take mayar da hankali wajen neman kakabawa kasashe masu tasowa ra’ayoyi da akidunta, ko da kuwa ba su dace da bukatu ko muradun wadancan kasashe ba. Amurka ta kan yi amfani da karfinta da tallafin da take ba kasashe masu karancin kudin shiga a matsayin wani makami na juya su yadda ta ga dama. Ta manta cewa, su ma ’yantattun kasashe ne dake da ikon cin gashin kansu da zartar da dokokin da suka dace da su.

Kasashen duniya sun bambanta da juna, al’adu ko addini ko kabila, ba za su taba zama iri daya ba. Kuma wannan bambancin shi ne ke kara kawata zaman rayuwa da koya mana yadda za mu zauna tare bisa girmamawa da hakuri da juna, kamar yadda shawarar kasar Sin ta wayewar kan duniya wato GCI ta gabatar, wato zaman jituwa da koyi da juna tsakanin mabanbanta al’ummomin duniya.  Kowace kasa a duniya na da ikon zabarwa kanta dokokin da suka dace da ita. Uganda ta zabi zartar da dokar hana auren jinsi, abun da ya kamata Amurka ta yi shi ne, girmama zabin Uganda, da kaucewa tsoma baki cikin al’amuranta na ci gida. Cire sunan wasu kasashe da ta yi daga yarjejeniyar AGOA ya nuna cewa, ba ci gabansu take nema ba kamar yadda take ikirari, cin zali da yadda za ta kasance mai babakere a duniya, shi ne burinta.

Amurka ta kan zartar da dokoki ko aiwatar da ayyuka, amma wadannan kasashe ba sa tsoma baki cikin al’amuranta, maimakon ta girmama ’yancinsu kamar yadda suke girmama ta, sai take amfani da karfinta wajen danniya da cin zali. A lokaci guda kuma, take ganin laifinsu da neman haddasa fitina a dangantakarsu da kasar Sin.

Sharadin huldar kasar Sin da kasashen ketare shi ne girmama juna da girmama cikakken ’yancin kasashe da moriyar juna ba tare da sharadi ba da kauracewa tsoma baki ko katsalandan cikin harkokinsu na gida, lamarin da ya sa take samun karbuwa a tsakanin kasashen duniya musamman masu tasowa.

Ya zama wajibi Amurka ta sake nazari ta sauya takunta domin kasancewarta daya tilo mai karfi a duniya, ba abu ne da zai yiwu ba, kana matakai maras dacewa da take dauka, suna kara rage kimarta a idon duniya.