Kashi 1 bisa 6 na baligan duniya na fama da matsalar rashin haihuwa
2023-11-06 11:35:08 CMG Hausa
Rahoton da hukumar lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta fitar a kwanan baya ya nuna cewa, kashi 17.5 cikin 100 na baligai a duniya suna fama da matsalar rashin haihuwa. Wasu daga cikinsu suna matukar alla-alla wajen kara samun hidimomin haihuwa masu inganci, wadanda za su biya kudi don samun biyan bukata.
Hukumar WHO ta amince da hakan bayan da ta tantance nazarce-nazarce 133 da aka gudanar a sassa daban daban na duniya daga shekarar 1990 zuwa ta 2021. Rahoton hukumar ya nuna cewa, a cikin kasashe masu yawan kudin shiga, kashi 17.8 cikin 100 na baligai na fama da matsalar rashin haihuwa, yayin da a cikin kasashe masu rauni da masu matsakaicin kudin shiga kuma, adadin ya dan ragu, inda ya kai kashi 16.5 cikin 100.
Mene ne ma’anar matsalar rashin samun haihuwa? Wannan na nufin, yadda ma’aurata ba sa samun haihuwa cikin tsawon shekara guda ba tare da daukar matakan hana daukar ciki ba. Akwai dalilai guda 2 da suka haifar da matsalar rashin haihuwar, ko dai matsalar a bangaren maza ne ko kuma mata.
A cewar jami’in hukumar ta WHO mai ruwa da tsaki, yadda baligai masu yawan haka ke fama da matsalar rashin haihuwa, ya shaida cewa, ana bukatar fadada ba da hidimomin haihuwa tsakanin mutane. Kana wajibi ne a tabbatar da ganin ana daukar batutuwa masu muhimmanci a fannonin nazarin harkokin kiwon lafiya da tsara manufofi. Ta haka mutanen da suke kokarin fatan samun ‘ya’ya, burinsu zai cika ba tare wata matsala ba ta hanyar da ta dace, kuma za su iya biyan kudi don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
La’akari da kalaman hukumar ta WHO, matsalar rashin samun haihuwa tana illanta lafiyar tunanin dan Adam, da sanya ana nuna musu bambanci, da kuma kawo wa wasu matsalar karancin kudi. Duk da haka ya zuwa yanzu ana fama da matsalar karancin kudade wajen yin rigakafin kamuwa da matsalar rashin haihuwa, da yanke hukunci kan kamuwa da matsalar da ba da jinya yadda ya kamata. Da yawa daga cikin wadanda suke fama da wannan matsalar, da wuya suke samun hidimomi masu ruwa da tsaki sakamakon makudan kudaden da ake kashewa, bambancin da ake nuna musu, da dai sauransu, ko kuma su zama matalauta sakamakon neman samun jinya. (Tasallah Yuan)