An bude bikin CIIE a Shanghai
2023-11-06 10:34:05 CMG Hausa
Aka kaddamar da bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na shida a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin. Bikin na bana, mai taken “more makoma tare a sabon zamani”, wanda ma’aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin gami da gwamnatin birnin Shanghai suka dauki nauyin gudanarwa, zai kammala ne a ranar 10 ga wata.