logo

HAUSA

A yi kokarin cimma burika a filayen gonaki

2023-11-06 15:40:37 CMG Hausa

Du Lizhi, mai ba da shawara kuma babbar ma’aikaciya ce a hukumar kula da harkokin gona da karkara ta Gaotang. Du ta ajiye littattafai 90 da take rubuta, inda take adana bayanai dangane da ayyukan da ta gudanar a sama da kauyuka 600 dake Gaotang, wata gunduma a birnin Liaocheng dake lardin Shandong na kasar Sin a shekaru 38 da ta shafe tana aiki. Idan kuka ji labarin Du mai taba zuciya, za ta burge ku saboda jajircewarta, musamman yayin da ta dage wajen cimma burinta na taimakawa manoma kyautata rayuwarsu.

An haifi Du Lizhi a shekarar 1964, kuma iyayenta manoma ne. A shekarar 1985, ta fara aiki a matsayin mai rike da fasahohin ayyukan gona a yankin Jiangdian na Gaotang. Shekaru 3 bayan nan, aka dauke ta aiki a hukumar kula da harkokin gona da karkara ta Gaotang.

A shekaru na farko-farko, ayyuka sun yi wa Du yawa. Da rana, ta kan ziyarci kauyukan Gaotang, domin ta lura tare da daukar bayanai game da yadda tsirrai suke girma. Da dare kuma, ta kan yi rubutu a littafinta, inda ta kan rubuta yadda ayyukanta suke gudana, kana ta kan karanta littattafai domin kara iliminta kan habaka ayyukan gona.

Du ta gamu da ruwan sama da dusar kankara sau da dama, haka zalika ta sha faduwa a kasa yayin da take duba tsirrai a gonaki. Du ta kara zage damtse wajen yin karatu saboda sakamakon da take samu daga bibiyar yanayin tsirrai, domin ta koyi fasahohin da ake bukata na kyautata aikin gona.

A matsyainta na ‘yar JKS kuma ma’aikaciyar kula da ayyukan gona, tana ganin ya zama wajibi ta taimakawa manoma warware matsalolin da suke fuskanta wajen habaka amfanin gona. A hankali ta zama kwararriya a fannin fasahohin aikin gona.

Du ta bayyana cewa, “Ina da alaka da manoma. Ina farin cikin taimakawa manoma shawo kan matsalolin da suke fuskanta a ayyukansu.”

Shekaru da dama da suka gabata, Kong Hejun, mazauniyar Kongzhang, wani kauye dake garin Gaotang, ta yi amfani da kudin da ta adana tsawon gomman shekaru da suka gabata yayin da take aiki a wani birni, domin kafa da raya babban filin gona. Da taimakon Du, Kong ta shuka alkama da masara da sauran tsirrai. Du ta kuma taimakawa Kong shawo kan wasu matsaloli masu bukatar fasaha a fannin gona. Bayan Kong ta samu amfanin gona mai armashi, karsashinta kan aikin gona ya karu.

“Ziyartar gonaki tare da tattaunawa da manoma akai-akai.” Wannan take, na hukumar kula da ayyukan gona ta Gaotang, ya nuna yadda aikin Du ke gudana. Duk da sauyin da ta samu daga mai tallafawa bunkasa ayyukan gona, zuwa shugabar tashar fasahohin ayyukan gona ta Gaotang, sannan kuma mataimakiyar daraktan ofishin kula da harkokin gona ta Gaotang, alaka mai karfi dake tsakanin Du da manoma ba ta sauya ba.

Tana shan aiki sosai, saboda yadda take samun gomman manoma dake buga mata waya a kullum. Bisa la’akari da karancin lokaci da karfi da ma albarkatu, Du ba za ta iya taimakawa kowanne manomi shawo kan matsalarsa ba. Ta riga ta nazarci yadda za ta magance matsaloli, don haka, dabararta ita ce, jagorantar dukkan ma’aikatan ofishin wajen yayata fasahohinsu ga manoma.

Cikin shekaru da dama da suka gabata, Du ta jagoranci abokan aikinta wajen gabatar da lakcoci da shawarwari ga manoma domin taimaka musu bunkasa fasahohinsu. Haka kuma, Du da abokan aikinta sun bude wani shafin yanar gizo, inda suka gabatar da bayanan da suka danganci aikin gona da fasahohi ga manoma.

Du ta kan karfafawa abokan aikinta gwiwar yin aiki tukuru, musamman domin inganta kwarewarsu, ta yadda mazauna kauyen za su kara aminta da su. Galibin abokan aikin Du sun zama hazikan masu tallafawa ayyukan gona kamarta.

“A ganina, a matsayin ma’aikaciyar kimiyya da fasahar aikin gona, gona ita ce dandamalina, kuma manoman ‘yan uwana ne. Na kan yi farin ciki da samun gamsuwa a duk lokacin da na taimakawa manoma magance matsalolin da suke fuskanta, ko kuma idan na ga sun samu kyautatuwar rayuwa,” cewar Du.

A shekarun baya bayan nan, raya sana’o’i irin na kauyuka, ya sanya aikin raya babban filin gona a fadin kasar Sin a kan gaba a fannin aikin gona na zamani. Manyan filayen gonakin suna kara sa kauyukan suna jan hankali, haka kuma suna karawa aikin gona kuzari. Har ila yau, suna karfafawa manoma gwiwar kara bayar da gudunmuwa ga aikin farfado da kauyuka.

An haifi Shi Chang a shekarun 1980, kuma tana zaune tare da iyalinta a Kaoshan, wani kauye dake birnin Harbin, hedkwatar lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin. A baya, Shi Chang ta yi aiki a shagon gyaran gashi har zuwa shekarar 2006, lokacin da ta yanke shawarar rufe shagon domin taimakawa iyayenta a aikin gona.

Domin bunkasa iliminta, ta shiga makarantar horar da fasahohin aikin gona, kuma a ko wace shekara ta kan ziyarci sauran yankunan kasar Sin domin nazartar dabarun raya ayyukan gona na yankunan. Cikin kankanin lokaci, Shi da iyalinta suka zama masu jagorantar sana’ar noma a kauyensu.

A shekarar 2013, aka zabi Shi a matsayin sakatariyar reshen JKS dake kauyen. A wancan lokaci, galibin mazauna kauyen sun manyanta. Haka kuma, ba a amfani da injuna sosai a aikin gona. Shi na son samo wani tsari, wanda zai dace da yanayin kauyen, da daga darajar aikin gona tare da taimakawa yankin inganta raya yankin.

Guan Fujun, mijin Shi ya iya sarrafa injuna sosai. Yayin da suke gudanar da bincike, Shi da Guan sun gano cewa, kasar kauyen za ta yi kyau da noman masara da waken soya da gero.

Shi ta tattauna sau da dama da jami’an kauyen game da raya kauyen. Daga bisani suka amince kauyen ya yayata babban filin gona a matsayin hanya mafi dacewa ta inganta ayyukan gona a yankin.

Saboda nasarar iyalin Shi a kan sana’ar aikin gona, iyalinta na daya daga cikin mutane na farko da suka kafa babban filin gona a kauyen.

Da farko, fadin gonar Shi, kadada 5 ne. Ta kan yi musayar fasahohi da jama’ar sauran kauyuka, kana ta kan taimaka musu ta hanyar sabunta fasahohinsu. A hankali a hankali, gonarta ta fara samun riba, lamarin da ya ja hankalin mutanen kauyen wajen hada gwiwa da gonar.

Yayin da aikin gona ya bunkasa, sai aka dauki tsari na bai daya na ayyuka da kula da gonaki, kana aka fara amfani da manyan injuna wajen shuka da girbi. Wannan ya taimaka wajen rage kudin da ake kashewa na gudanar da ayyuka, wanda kuma ya taimaka wajen samun karuwar riba.

Iyalin Shi sun kasance masu bayar da muhimmanci ga ingancin amfanin gona. Su kan bata lokaci wajen zabar ire-iren da suka dace, sannan su kan mayar da hankali kan kula da gonaki, musamman yaki da kwari.

Kwalliya tana biyan kudin sabulu dangane da aiki tukuru da suke yi. Yanzu iyalin Shi na da gonar da ta kai fadin kadada 2,000, haka kuma tana samar amfanin gona mai armashi, domin ana samun ton 20,000 na masara a ko wace shekara. Daruruwan mata ne ke shiga harkar gona a ko wace shekara. Har ila yau, Shi na taimakawa mata noman kayan lambu. Kudin shigar mazauna kauyen ya karu a shekarun baya-bayan nan.

A shekarar 2020, aka ayyana Shi Chang a matsayin wadda ta fi kowa samar da masara a lardin Heilongjiang. Ta kuma samu lambar yabo ta mata mafi nagarta ta lardin da kuma lambar yabo ta kasa ta mata ababen koyi saboda nasarorinsu. A watan Mayun shekarar 2023, aka ayyana iyalin Shi Chang a matsayin kyakkyawan iyali na kasa. (Kande Gao)